Protonmail ya biya masu satar bayanai kudin fansa

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shafin internet na Protonmail na kasar Switzerland ya bayar da sama da fam 3,600 a matsayin kudin fansa ga masu satar bayanai bayan harin da aka kai wa shafinsa.

Masu satar bayanai sun ce kudin zai sa su daian kai wa shafin hari.

Sai dai duk da cewa kamfanin bayar da kudin fansar kawo yanzu masu satar bayanai na ci gaba da kai masa hari.

A yanzu kamfanin ya kaddammar da asusun neman kudi domin tara isasun kudi da zai bashi damar shawo kan hare hare makamantan wannan nan gaba.

Harin farko da aka kai wa kamfanin ya shafi ayuikansa har na tsawon mintuna 15 sai dai an sake kai masa hari washe gari