Biafra: Ana ci gaba da zanga-zanga

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Masu neman ballewa daga Nigeria

Daruruwan mutane a kudu maso yammacin Najeriya ne ke zanga zanga a kan ci gaba da tsare wani mai fafutukar kafa kasar Biafra.

A watan jiya ne aka kama Nnamdi Kanu, wanda shugaban gidan radiyon Biafra ne.

Gwamnati ta ce gidan rediyansa na aiki ne ba tare da lasisi ba.

An kwashe shekara biyu da rabi ana yakin basasa da masu neman kafa kasar Biafra wanda ya kare a shekarar 1970.

Sama da mutane miliyan daya ne suka rasa rayukansu dayawansu sakamakon yunwa da cutuka, kafin sojoji su kawo karshen tada kayar bayan.