Buhari ya nada sabbin manyan sakatarori

Image caption Buhari ya yi alkawarin kawar da cin hanci da rashawa

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori a ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Sabbin manyan sakatarorin 18 za su kama aiki nan take.

Hakan na zuwa ne bayan da shugaba Buhari din ya kori wasu manyan sakatarori 17 daga bakin aiki.

Sanarwa daga fadar shugaban kasar ta ce, shugaba Buhari ya kuma sauyawa wasu manyan sakatarorin wuraren aikinsu.

Sabbin manyan sakatarorin su ne;

 1. Mrs. Ayotunde Adesugba
 2. Alhaji Mahmoud Isa-Dutse
 3. Mr. Taiwo Abidogun
 4. Dr. Bukar Hassan
 5. Mrs. Wakama Belema Asifieka
 6. Mr. Jalal Ahmad Arabi
 7. Mr. Sabiu Zakari
 8. Mrs. Obiageli Phyllis Nwokedi
 9. Mr. Aminu Nabegu
 10. Mr. Bamgbose Olukunle Oladele
 11. Mr. Alo Williams Nwankwo
 12. Dr. Shehu Ahmed
 13. Mr. Ogbonnaya Innocent Kalu
 14. Mrs. Nuratu Jimoh Batagarawa
 15. Mr. Christian Chinyeaka Ohaa
 16. Mr. Bassey Apkanyung
 17. Mr. Louis Edozien
 18. Dr. Ugo Roy