Ko me yasa matan Habasha suka rage haihuwa?

Wa ta Uwa a kasar Habasha
Image caption Mata na kara wayewa wajen amfani da maganin tsarin iyali.

A kasar Habasha an samu raguwar yawan haihuwa, inda ake samun mace ta haifi 'ya'ya bakwai a shekarun 1990, amma a yanzu ba sa wuce 'ya'ya hudu zuwa shida. Shin ko ta yaya suka yi irin wannan kokarin?

Kasar ta samu wannan sauyi ne sakamakon wasu abubuwa.

Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta asusun yawan al'umma a kasar Habasha, Fausin Yao ta ce ''Mata na dadewa a makaranta, tsadar rayuwa na karuwa, dan haka mutane ba sa son haifar 'ya'ya da yawa, muhimmi shi ne mutane sun waye da yin tsarin iyali.''

Tattalin arzikin kasar na daga cikin wanda ke bunkasa cikin sauri a duniya, a daidai lokacin da rayuwa ke kara tsada, mutane sun gwammace su haifi 'ya'ya kalilan.

Muluwork Tesfaye ma'aikaciyyar jiyya ce a wani asibiti a birnin Addis Ababa, ta ce ba za ta iya kula da 'ya'ya da yawa ba a birnin ba.

Tesfaye dai su takwas ne a gidansu, kuma iyayen ta sun yi ta fadi-tashi dan kulawa da su.

Ta ce ''Miji na shi ne ya sanya ni makaranta, dan haka ni ma ina son 'ya'ya na su samu ingantacciyyar rayuwa''.

Image caption An samu raguwar yawan haihuwa a kauyukan kasar Habasha.

'Tsarin iyali'

Samun maganin tsarin iyali a saukake, na taimakawa wajen rage yawan haihuwa a kasar Habasha.

Wani rahoto da Asusun yawan al'umma na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar ya gano cewa, yawan shan maganin tsarin iyali da aka yi tsakanin shekarun 2000 zuwa 2011 ya taka muhimmiyar rawa wajen rage haihuwa a kasar.

Amma duk da hakan, yawancin mata ba su samu damar yin amfani da wannan magani ba.

Haka kuma an samu raguwar yawan haihuwa a yankunan karkara.

Anyenalem Daw, uwa ce mai shekaru sama da talatin da take da 'ya'ya shida, da ke zaune a kauyen Weyo Rafu Hargisa mai tafiyar sa'o'i hudu daga birnin Addis Ababa.

Ta ce inda ta samu labarin maganin tsarin iyali, da 'ya'ya hudu kadai za ta haifa.

Ta kuma ce mata a kauyensu su kan gudanar da wani taro da suke kira ''Shene'', domin tattaunawa a kan tsarin iyali da batutuwan da suka shafi lafiya.

''Abubuwa su na sauyawa, ina ganin yara na za su haifi 'ya'ya bibbiyu ne,'' In ji Misis Anyenalem.

Jami'an lafiya na gabatar da kaloli daban-daban a kauyuka, dan wayar da kan matan da suke son sanin wani bayani game da tsarin iyali.

Image caption Manyan malaman addinai biyu a kasar Habasha ba su fito sun nuna goyon bayan yin tsarin iyali ba.

Rarraba maganin tsarin iyali da jami'an lafiya suka yi a kauyuka a shekarar 2000 zuwa 2011, shi ma ya taimaka wajen rage yawan haihuwar.

Wannan ma ya taimaka matuka wajen karuwar yara mata da ke zuwa makaranta.

To sai dai kuma manyan addinnan kasar Habasha watau addinin Musulunci da Kiristanci na gargajiya, ba su fito fili sun nuna amincewa da tsarin iyali ba, amma su jami'an lafiyar sun ce shugabannin addinnan na goyon bayan ayyukan da su ke yi.

Kasar Habasha dai na daga cikin kasashen Afirka Tara da yawan al'ummar ta ke raguwa.