Taswirar Google za ta yi aiki ko ba intanet

Hakkin mallakar hoto Here
Image caption Taswirar ta Google za ta yi aiki ko ba intanet.

Google ya kara gyara manhajar taswirarsa wato google maps domin sanya mutane a hanya ko da kuwa ba bu intanet.

Sabuwar manhajar dai za ta ba wa masu ta'ammali da ita damar gano wuraren sana'o'i da lokacin da ake bude su har ma da lambar wayoyinsu, ba tare da intanet ba.

Kamfanin na google ya ce 'yan yawon bude ido da kuma mutanen kasashen da amfani da intanet yake da tsadar gaske za su iya cin gajiyar wannan sabon tsari.

Amma kafin ayi amfani da wannan tsarin sai an nemo yankin da mutum yake.

Kuma da zarar an zabi yanki, manhajar za ta juya kai tsaye daga yanayin tsarin intanet zuwa maras intanet.

Hakan kuma yana nufin alal misali idan matukin mota ya fara balaguro daga garejin gidan kasa ba tare da tsarin intanet ba, manhajar za ta zaba masa hanyar da zai bi da tsawon lokacin da zai dauka.

To amma kuma daga bisani manhajar za ta yi wasu 'yan gyare-gyare idan a kan hanyar da ta zaba wa direban akwai cunkoson ababan hawa ko kuma hadari.

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Masu yawon bude da wadanda a garuruwansu akwai tsadar intanet za su fi cin gajiyar taswirar.

Taswirar ta google za ta rinka sabunta kanta a duk tsawon kwanaki 15 domin dace wa da yanayi, idan har an jona waya domin yin caji sannan kuma ta samu jonin tsarin intanet na Wi-fi, sai dai idan mai amfani da wayar ba ya son hakan.