Sall ya soki 'tsattsauran ra'ayin' Musulunci

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Sall na son mutane su fahimci tsarin Musulunci

Shugaban Senegal, Macky Sall ya yi kira a yaki 'tsattsauran ra'ayin' addinin musulunci, abin da ya ce yake janyo karuwar kungiyoyin masu jihadi.

A cewarsa, akwai bukatar a horas da malaman addinin musulunci domin su koyar da yin abubuwa na girmama addinin musulunci.

Mr Sall wanda shi ma Musulmi ne, ya kuma yi kira a da a yi musayar bayannan sirri tsakanin gwamnati da malamai domin cimma burin da aka sa a gaba.

A jawabinsa a wajen taro kan zaman lafiya da tsaro a Dakar, Mr Sall ya ce al'umma na bukatar a basu kwarin gwiwa domin 'kawar da ra'ayin Musulunci' mai tsauri.

A makon da ya gabata ne hukumomi a Senegal suka tuhumi Limamai biyu bisa zargin halasta kudaden haramun da kuma alaka da kungiyoyin masu tayar da kayar baya.