Shekaru 20 da rasuwar Saro Ken Wiwi

Ken Saro Wiwa Hakkin mallakar hoto Greenpeace
Image caption An kashe mai fafutukar ne shekaru Ashirin da suka gabata.

A Najeriya ana gudanar da addu'o'in cika shekaru ashirin da zartar da hukuncin kisa kan mai fafukar nan kuma marubuci Ken Saro Wiwa.

An kashe Mista Wiwa tare da wasu mutane takwas ,wadanda suka dade suna gangamin kin amincewa da hayaki mai gurbata muhalli da kamfanin mai na Shell ke haddasawa a Ogoni da ke yankin Niger Delta mai arzikin mai a kasar.

Kasashen duniya sun yi Allah-wadai da kisan nasu, inda har hakan ya janyo aka cire Najeriya daga kungiyar Commonwealth.

A makon da ya wuce hukumar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International, ta zargi kamfanin mai na Shell da gaza share dagwalon mai a yankin na Ogoni, zargin da Shell ya musanta.