BH: Sojojin kasashe 5 za su fara aiki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Najerya

Ministan harkokin wajen Chadi ya ce rundunar hadin gwiwa ta kasashe biyar da aka kafa don yaki da kungiyar Boko Haram za ta fara aiki a watan Janairun badi.

Mista Moussa Faki ya sanar da hakan ne a Dakar, inda yake halartar wani taro kan zaman lafiya a Afirka.

Ya ce akwai matsalar rashin kyawun yanayi, saboda damuna, don haka sojoji ba za su fara aiki ba har sai watan Janairu.

Game da kudaden tafiyar da rundunar ta hadin gwiwa, Mista Faki ya ce Nijeriya ta ce za ta samar da dala miliyan 100, baya ga kudaden da sauran kasashen za su hada.

Sannan kuma ana sa ran samun tallafi daga Tarayyar Afirka, da Tarayyar Turai, da kuma wasu kungiyoyin kasa da kasa da wasu kasashe da suka sanar da cewa zasu taimaka wa wannan runduna.