Ana taro kan 'yan ci-ranin Afrika

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daruruwan 'yan ci-rani na neman mafaka a Turai

Shugabannin Turai da Afirka na taro a tsibirin Malta domin tattaunawa a kan yadda za'a tsaida kwararar 'yan ci-rani 'yan Afirka da ke zuwa Turai.

An kafa wani asusu a kusan Euro biliyan biyu domin tallafawa mutane da su zauna a nahiyarsu.

A Slovania, mahukunta na gina wata katanga a kan iyakarta da Croatia, domin rage kwararar 'yan gudun hijirar da ke nausawa arewacin Turai.

A 'yan makonnin da suka wuce kimanin 'yan gudun hijira dubu dari da tamanin ne suka shiga Slovania.

Wasu karin 'yan gudun hijirar sun rasa rayukansu a kokarin zuwa Turai.

Mutane goma sha hudu --- cikinsu kananan yara bakwai -- ne suka nutse a cikin jirgin ruwan da ya dakko su gada Turkiyya zuwa tsibirin Lesbos na kasar Girka.