'Yan adawa sun lashe zaben Myanmar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jagorar 'yan adawa Aung San Suu Kyi

Wani kakakin shugaban kasar Myanmar, Thein Sein, ya ce yana san ya taya jagorar 'yan adawa Aung San Suu Kyi murna a kan nasarar da suka samu a zaben da aka yi ranar Lahadi.

Jam'iyyar NLD ta samu kusan kashi casa'in cikin dari na kujerun majalisar da aka bayyana kawo yanzu.

Ms Suu Kyi ta aike wa shugabannin da sojoji ke goyan baya wasikar gayyatar tattaunawa a kan sasantawa a kasar.

Kakakin shugaban kasar, ya fada wa BBC cewa ba'a jinkirta bayyana sakamakon zaben ba da gangan kuma a shirye ya ke ya yi ganawar bayan an bayyana sakamako na karshe.