PDP ta nemi afuwar 'yan Nigeria

PDP
Image caption Jam'iyyar PDP ta amince da gaza cimma bukatun al'umar Najeriya.

Babbar jam'iyyar Adawa ta PDP a Najeriya, ta nemi afuwar 'yan kasar wajen gaza cimma bukatunsu har tsahon shekaru 16 da ta yi a karagar mulkin kasar.

Jam'iyyar ta ce, tsaida tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar su a shekarar 2015 babban kuskure ne.

Shugaban kwamitin tsare-tsare na taron Dr Reymond Dokpesi shi ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka yi a ranar Talata a Abuja.

Ya kara da cewa, sun san 'yan Najeriya na jin haushi saboda wasu matakai da suka dauka a lokacin da suke mulki.

PDP ta ce a shirye ta ke ta gyara kura-kuranta, dalilin da ma ya sa ta ke shirya wani babban taro da za a tattauna matsalolin da aka samu a waccan gwamnatin.

Shan kayen da PDP ta yi a zaben da ya gabata dai ya baiwa shugabannin jam'iyyar mamaki.

Baya ga rasa kujerar shugabancin Najeriya da PDP ta yi, inda jam'iyyar APC ta samu nasara, hatta a wasu jihohin kasar da a da can ta ke gwana ta sha kaye.