Abokan hammaya sun soki Donald Trump

Donald Trump

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Donald Trump

Abokan hammaya da ke neman takarar shugabanci Amurka karkashin inuwar jam'iyyar Republicans sun yi kakkausan suka ga shirin Donald Trump na kwashe 'yan cirani kusan miliyan 11 domin mayar da su zuwa kasashensu.

Sun bayana haka ne wata mahawara ta baya bayan nan da kafar talabajin na Fox Business ta watsa a Milwaukee

'Yan takarar sun kuma tattaunawa a kan batutuwa da suka shafi tsarin albashi mafi karanci da yankin gabas ta tsakiya.

Wannan shi ne karo na hudu da 'yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta Republicans su takwas zasu fafata da juna a garin Milwaukee.