Rasha za ta yi bincike kan amfani da kwayoyi

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Shugaban Rasha Vladimir Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya sha alwashin magance matsalar masu shan kwayoyi masu kara kuzari a fagen wasanni a kasar.

Shugaban ya yi alkawarin ne bayan an zargi wasu 'yan wasan kasar da amfani da magungunan kara kuzari.

Da yaka jawabi bayan ya gana da manyan jami'an da ke kula da wasanni a kasar, Shugaba Putin ya ce kasar sa za ta yi dukkan mai yiwuwa wajen kawo karshen amfani da magunguna masu kara kuzari a sha'anin wasanni.

Wannan shi ne kalaminsa na farko tun bayan da hukumar da ke yaki da amfani da magungunan kara kuzari a wasanni ta fitar ranar Litinin, tana mai bayyana wani shiri da ta ce ya samu goyon bayan gwamnati, kan yadda za a hana 'yan wasa amfani da magungunan kara kuzari.

Mista Putin ya ce dole ne ita ma Rasha ta gudanar da na ta binciken game da zarge-zargen, sannan kuma ya ce ba kasarsa ce kawai ke fama da matsalar ba.