'Yan sanda za su sha dauri a Afrika ta kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mido Macia a lokacin da 'yan sanda ke jansa zuwa ofishinsu

Wani alkali ya yanke wa wasu 'yan sanda takwas hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekaru goma sha biyar saboda kisan wani direban Tasi dan kasar Mozambique.

An kashe mutumin mai suna Mido Macia a shekarar 2013 bayan da 'yan sandan sun daure shi a bayan motarsu.

An same shi cikin jini a wajen 'yan sandan.

Alkalin Bert Bam ya kira kisan a matsayin tsabar rashin imani, amma ya ce ba da niyya aka yi ba.

Lauyan da yake kare 'yan sandan ya ce za su daukaka kara a kan hukuncin da aka yanke musu.

'yan sandan sun kama direban Tasin ne saboda zarginsa da laifin ajiye mota ba a inda yakamata ba.

Daga nan sai suka kama shi suka tafi da shi ofishinsu, a nan ne kuma aka samu gawarsa sakamakon raunukan da ya samu a ka.