'Sojojin Kenya na gudanar da haramtaccen ciniki'

Hakkin mallakar hoto AP

Wata kungiyar kare hakkin ma'aikata a Kenya ta zargi sojojin kasar da hannu a wani haramtaccen ciniki da kuma keta hakkin dan- adam a Somalia

Kungiyar mai suna Jounalist for Justice, tace dakarun tsaron Kenya na samun kusan dala miliyan hamsin a shekara daga harajin da suke karba wajen fitar da gawayi daga Somalia da kuma sukari idan ya shigo cikin kasar.

A lokaci guda kuma, kungiyar ta bayyana yadda hare- haren saman sojojin kasar Kenyan wanda sojojin ke cewa ana harar mayakan al-shabab-- ke lalata kauyukan Somalia da wuraren da ake samun ruwa da kuma kashe dabbobi

Sai dai Sojojin Kasar Kenyan sun musanta wadannan zarge zarge