Dakarun Kurdawa na yunkurin kwace Sinjar

Hakkin mallakar hoto reuters
Image caption Dubban Yazidawa ne suka makale a garin na Sinjar.

Dakarun Kurdawa a arewacin Iraki sun kaddamar da hare-hare a yunkurin da suke yi na sake karbo garin Sinjar mai matukar muhimmanci, wanda ke kan iyakar Syria, daga hannun 'yan kungiyar IS.

Gamayyar kasashen da Amurka ke jagoranta na taimaka musu ta hanyar kai hare-hare ta sama.

Idan dai aka sake kama garin na Sinjar, za a hana 'yan kungiyar IS da ke yankin Raqqa da na Mosul ganawa da juna.

Dubban mabiya addinin Yazidi da ba su da rinjaye ne suka makale a garin lokacin da suka tsere kan duwatsun da ke Sinjar bayan dakarun IS sun kwace garin a bara.

An kashe daruruwan mutane, akasarinsu maza, sannan aka rika yin lalata da mata mabiya Yazidi.

Hare-haren da ake kai wa a kan garin Sinjar na daya daga cikin dalilan da suka sa Amurka ta fara kai hare-hare ta sama a yankunan da ke hannun kungiyar IS a Iraki a watan Agustan shekarar 2014, a daidai lokacin da ake ta gargadin cewa ana yin kisan kare-dangi a garin.