Saraki ya yi nasara a Kotun Koli

Image caption Ana tuhumar Saraki da laifin yin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Kotun Kolin Najeriya ta dakatar da shari'ar da kotun da'ar ma'aikata ke yi wa shugaban majalisar dattawan kasar, Bukola Saraki.

Kotun ta ce ta dauki matakin ne saboda Bukola Saraki ya shigar da kara a wajenta, inda yake son sanin ko kotun da'ar ma'aikatan tana da hurumin yi masa hukunci.

A cewar Kotun, sai ta kammala sauraren wannan kara tukunna gabanin a sani ko za a iya ci gaba da yi wa Saraki shari'a a kotun da'ar ma'aikatan.

A kwanakin baya ne shugaban majalisar dattawan ya kai kotun da'ar ma'aikatan kara, inda ya bukaci a yi masa bayani kan ko kotun da'ar ma'aikata tana da hurumin yi masa shari'a ko kuma a'a.

Kotun da'ar ma'aikatan dai tana tuhumar Bukola Saraki ne ne da laifuka goma sha uku, wadanda ke da alaka da yin karya wajen bayyana kadarorinsa a lokacin yana gwamnan jihar kwara.

Sai dai Mr Saraki ya musanta dukkanin zargin da kotun da'ar ma'aikatan ke yi masa.