Ana makokin mutane 40 da aka kashe a Beirut

Hakkin mallakar hoto Reuters

An soma makoki a Beirut babban birnin Kasar Labanon bayan wasu tagwayen boma bomai da suka yi sanadiyyar rayukan mutane fiye da 40 da kuma jikkata kusan mutane 100.

Kungiyar da ke da'awar kafa daular musulunci ta IS ta ce ita ta kaddamar da hare haren.

An kai hare haren ne a wata unguwa ta 'yan Shi'a, a wani titi mai cike da hada hada.

Wadannan sune hare- haren bom mafi muni da aka gani a Beirut, tun lokacin da aka kawo karshen yakin basasar Labanon a shekarar 1990