An daƙile harin 'yan Boko Haram a Gwoza

Hakkin mallakar hoto nigerian army
Image caption Sojojin sun ce sun kwato makamai da dama.

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun yi artabu da mayakan Boko Haram lokacin da 'yan kungiyar suka yi yunkurin kai hari kan sansanin sojin da ke garin Gwoza na jihar Borno ranar Juma'a.

Kakakin rundunar sojin kasar, Sani Kukasheka Usman, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce soji sun kashe 'yan Boko Haram bakwai, a fafatar da suka kwashe sa'oi biyu suna yi.

Ya kara da cewa, dakarunsu sun kwato mota kirar Toyota guda daya, da bindigogi kirar AK-47 goma sha daya, da bindigar Shilka daya, da bindigar harbo jiragen sama guda daya da gurneti shida da alburusai da dama.

A cewar sa, dakarun sojojin sama na ci gaba da yin luguden wuta kan 'yan Boko haram din da ke yunkurin komawa dajin Sambisa da zummar murkushe su.