Mutanen da suka mutu a Paris sun kai 40

Image caption Daya daga cikin wuraren da aka kai hari a Faransa

'Yan sanada a Faransa sun ce akalla mutane 40 ne suka mutu a wasu hare hare da aka kaddamar a Paris.

Rahotanni sun ce an yi harbe harbe a akalla wurare biyu a arewa maso gabashin babban birnin kasar.

An kuma samu fashewar wasu abubuwa a filin wasa na kasar inda shugaba Francois Hollande ke kallon wasan kwallon kafa tsakanin kasarsa da Jamus.

An fitar da shugaba Hollande daga filin wasan, sannan aka dakatar da wasan.

Wakilin BBC ya ce ya ga gawarwaki a kwance a kusa da wani gidan sayar da abinci

Wasu rahotannin na cewa an yi harbe harbe a wani gidan rawa dake gunduna ta 11 a birnin Paris, sannan kuma a na ganin an yi garkuwa da akalla mutane 60.

Wakilin wani gidan talabijin a Faransa ya ce an harba gurneti da dama a filin wasan, kuma mutane da yawa a nan ma sun mutu.

Shugaba Obama na Amurka ya yi Allah wadai da hare-haren, sannan ya sha alwashin hada kai da Faransa don gano wadanda ke da alhaki, tare da hukunta su