An janye motar Google daga hanya a California

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Mota mai tuka kanta kirar Google

'Yan sanda a yankin Mountain View na California sun janye wata mota mai tuka kanta daga kan hanya, wadda kamfanin Google ya kera saboda tana tafiya a hankali sosai.

Babu wani mataki da 'yan sandan suka dauka a kan motar, sai dai lamarin, ya janyo tambayoyi kan ko ire-iren motocin sun cika takatsantsan ne.

Wani rahoto kan hadururrukan motoci da ma'aikatar kula da sufuri a California ta fitar ya bayyana motoci masu tuka kansu kirar kamfanin Google a matsayin wadanda suka cika takatsantsan.

A bayanan da ta wallafa a shafinta na intanet, hukumar 'yan sanda ta yankin Mountain View ta ce wani jami'inta ya lura da yadda motoci ke cunkushewa a kan hanya sakamakon rashin saurin motar kirar Google.

"Hakan ne ya sa jami'in ya tsayar da motar, ya kuma tuntubi masu kula da ita don fadakar da su irin saurin da ake bukata motar ta yi a kan hanyar da kowa ke bi, don gudun hada cunkoso" hukumar 'yan sandan ta ce.

A watan Satumba, kanfanin Google ya ce ya na kokarin ganin motocin da yake kerawa masu tuka kansu suna tafiya kamar mutane ke tukasu, saboda korafin da wasu ke yi akan cewa motocin sun cika tafiya a hankali.