Niger: Hukumomi sun cafke Hama Amadou

Hakkin mallakar hoto

A Jamhuriyar Nijar hukumomin kasar sun kama tsohon kakakin majalisar dokoki Malam Hama Amadou jim kadan bayan saukar sa a filin jiragen saman kasar na Diori Hamani daga kasar Faransa inda yake gudun hijira sama da shekara daya.

Rahotanni dai na cewa tuni aka kai shi gidan kason Filinge da ke da nisan kilomita 180 arewa maso gabashin Yamai.

A can baya dai hukumomin kasar na zargin Malam Hama Amadou ne da hannu a wata badakalar cinikin jarirai daga Najeriya zuwa kasar ta Nijar, zargin da ya musanta yana mai cewa bita da kullin siyasa ce.

Jami'an tsaro sun fesa barkonon tsohuwa a kan magoya bayansa da suka je tarbarsa

Rahotanni na cewa an tsaurara matakan tsaro a birnin Yamai na jamhuriyar Niger tun a ranar Asabar.