Mummunan hadarin jirgin kasa a Faransa

Jirgin TGV na Faransa da ya yi hadari
Image caption Jirgin TGV na Faransa da ya yi hadari

Mutane akalla 10 ne suka rasu wasu goma sha dauya kuma suka sami raunuka yayinda wani jirgin kasa mai tsananin gudu ya goce daga layin dogo a gabashin Faransa.

Jirgin na TGV yana gwajin sabon layin dogo ne tsakanin Paris da Strasbourg.

Ya goce daga kan hanyarsa ne Eckwersheim kusa da kan iyaka da Jamus, ya kuma rabe gida biyu.

An gano wasu tarkacen jirgin a wata korama.

Jirgin na dauke ne da mutane 49 kuma dukkaninsu ma'aikata ne masu gyaran jirgi.

Jami'ai a yankin sun ce sun yi imani jirgin ya na gudun da wuce kima.

Wannan dai shine hadari mafi muni na jirgin TGV a cikin fiye da shekaru talatin.