Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Faransawa sun kwana cikin zulumi

Wata kungiyar mawaka ta California ta na nishadantar da mutanen da suka cika a Bataclan inda ake gudanar da wasannin lokacin da maharan suka afka suka kuma bude wuta a kan cincirindon jama'ar.

Mutane tamanin suka rasu a nan.

An tura dakarun kundunbala domin shawo kan lamarin.

An jiwo amon harbe harbe yayin da jama'ar da suka halarci wasannin suke ta neman tsira da rayukansu.