Amirka ta kashe shugaban IS a Libya

Jirgin yakin Amirka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin yakin Amirka

Wani mai magana da yawun hukumar tsaro ta Pentagon yace kashe Abu Nabil zai dakushe tasirin ISIS na cimma burinta a Libya.

Abu Nabil wanda dan asalin Iraqi ne ya zama shugaban kungiyar ISIS a Libya bayan zama mayaki a kungiyar Al Qa'ida tsawon shekaru da dama.

Hukumar tsaron Pentagon ta ce mai yiwuwa shine ya yi magana a wani faifan bidiyon da ya nuna kisan wasu Kiristoci yan Coptic a Libya a farkon wannan shekarar.