Faransa:'Yan sanda na neman dan bindiga

Abdeslam salah dan bindigar da ake nema ruwa a jallo Hakkin mallakar hoto pa
Image caption Abdeslam salah dan bindigar da ake nema ruwa a jallo

Jami'an Faransa sun ce suna neman wani mutum ruwa a jallo wanda ake kyautata tsammanin yana da hannu a hare haren kunar bakin wake da aka kai a Paris a ranar Juma'a.

Sun bukaci jama'a duk wanda ya ga mutumin mai suna Salah Abdelsalam mai shekaru 26 kuma haifaffen Brussel ya sanar da hukuma.

Yana daya daga cikin yan uwa su uku wadanda aka yi imanin suna da hannu a hare haren, an harbe daya a gidan rawa na Bataclan yayin da aka kama wani a Belgium.

Ministan cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve yace wasu mutane ne suka tsara harin a Belgium tare da goyon bayan wasu a cikin Faransa.