Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tattalin arzikin Najeriya na tangal-tangal

Hakkin mallakar hoto
Image caption Faduwar farashin mai a kasuwannin duniya ya janyo tattalin arzikin Najeriya fuskantar koma baya.

A Nigeria, Masana tattalin arzikin kasa na cewa faduwar farashin man fetur a kasuwannin duniya ya shafi tattalin arzikin Najeriyar da kuma darajar kudin kasar.

Sai dai wasu na ganin tsawon lokaci da gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka ba tare da nada ministoci ba, ya taimaka kasar ta gaza samun alkibla da za ta kaita ga samun mafita. ga rahoton da Umar Shehu Elleman ya hada mana.