Paris: An bayyana sunan mahari daya

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Jami'in dan sanda a Paris

Masu bincike a Faransa sun bayyana sunan daya daga cikin mutane 7 da suka kaddamar da munanan hare hare a Paris da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 129.

An bayyana Umar Isma'il Mostefai, wani Bafaranshe mai shekaru 29, ta hanyar amfani da dan yatsarsa da aka gano a wurin da maharan suka fi kashe mutane.

Mostefai mutun ne dake da tarihin zama bata gari, kuma mai son rungumar tsatssaurar akidar Musulunci.

'Yan sanda na kokarin gano ko mutumin ya taba zuwa Syria.

Masu shigar da kara na gwamnati sun ce maharan, dauke da bindigogin AK47 da rigunan kunar bakin wake, sun raba kansu zuwa gida uku, kuma ana fargabar ko wasun su sun samu tsarewa.