EU:Ba bukatar sauya dokoki kan yan gudun hijira

Shugaban hukumar tarayyar turai Jean-Claude Juncker Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban hukumar tarayyar turai Jean-Claude Juncker

Mr Juncker yana magana ne a Turkiya a taron kungiyar G20, yace mutanen da suka aikata ta'asar hari a Paris miyagun mutane ne ba yan gudun hijira ba ne.

Hukumomi a Faransa sun baiyana daya daga cikin maharan da cewa dan kasar Syria ne wanda ya shiga cikin turai ta kasar Girka makonni shida da suka wuce.

A halin da ake ciki, Jami'ai a Poland da Slovakia sun ce ba za su aiwatar da yarjejeniyar tarayyar turai ta tsugunar da dubban yan gudun hijira wadanda suka fito daga Afirka da gabas ta tsakiya a watannin baya bayan nan ba.