Obama da Putin sun gana a taron G20

Putin da Obama Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Putin da Obama

Fadar gwamnatin Amirka ta ce shugabannin biyu sun amince cewa hare haren da suka faru a Paris sun karfafa bukatar sulhunta rikicin Syria cikin gaggawa.

Sun kuma ce akwai bukatar tsagaita wuta da kaddamar da shirin mayar da kasar kan turbar siyasa.

Mr Obama ya yi maraba da yunkurin kasashe na tunkarar kungiyoyin yan bindiga da masu da'awar jihadi, ya kuma bukaci Rasha ta mayar da hankali a kan IS a farmakin da ta ke yi a Syria.

Tun farko shugaban hukumar tarayyar turai Donald Tusk yace ruwan bam abamai da Rasha ke yi a kan yan adawa masu sassauci ra'ayi a Syria ya na yawan yan gudun hijira da ke kwarara zuwa kasashen turai.

Mr Tusk yace matakin soji da Rasha ke yi a Syria, ya kamata ya maida hankali ne akan mayakan IS, kuma akwai bukatar Rasha da Amirka su hada hannu a yakin da suke yi da kungiyar.