Ranar tunawa da wadanda suka yi hadari

Hadarin motar safa
Bayanan hoto,

Hadarin motar safa

Ranar 15 ga watan Nuwamba, ranar tunawa da mutanen da haduran ababen hawa suka rutsa da su a duniya.

Majalisar Dinkin Duniya da kuma wata kungiya mai fafutikar kiyaye hadura da taimaka wa wadanda hadura suka rutsa da su ta kasar Birtaniya mai suna, RoadPeace, ne suka kebe ranar a duk shekara.

An kebe ranar ce da nufin yin waiwaye game da wadanda suka jikkata, ko suka rasa rayukansu, a haduran ababen hawa, da kuma duba halin da 'yan uwa da abokan arzikinsu suka shiga sanadiyar hakan.

Nijeriya dai ita ce kasa ta biyu mafi yawan samun hasarar rayuka da jikkata sanadiyar haduran hanyoyin mota, bayan kasar Indiya inda dubban mutane kan rasa rayukansu a duk shekara a cewar wasu alkaluma na Hukumar Lafiya ta Duniya.

Manazarta dai na danganta yawaitar hadura a hanyoyi ne da tukin ganganci mo cikin maye, da lafta kaya fiye da kima, da rashin lafiyar abin hawa, da rashin kyawun hanya, da daoi sauransu.

Yayin da ake gudanar da hidimar ranar tunwa da wadanda haduran hanyar, suka rutsa da su a duniya, fatan da masu ruwa da tsaki ke bayyana shi ne a samu raguwar hadarun, da kuma kara himma wajen ceto rayukan jama'a a hanyoyin mota.