An kama 'yan Boko Haram a Senegal

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Macky Sall na Senegal ya sha alwashin yaki da masu tsattsaura ra'ayi.

Hukumomi a kasar Senegal sun ce sun kama mutane da dama da ke da alaka da kungiyar Boko Haram.

Hukumomin sun ce an kama mutanen ne a cikin makonni biyun da suka wuce.

Daga cikin wadanda aka kama dai har da wasu mata guda biyu da kuma wasu wadanda ake tuhuma da yin shigar mata.

Haka kuma an kama wata 'yar uwar wani dan Boko Haram a Najeriya wadda jami'an tsaro suka ce tana musayar kudade tsakaninta da dan Boko haram din.

Senegal dai ta kasance kasa mai rinjayen musulmi wadda ta yi fice ta fannin zaman lafiya.

A baya-bayan nan ne dai shugaban kasar, Macky Sall ya ayyana yaki da masu tsattsuran kishin addinin Islama.