An lalata wurin ƙera makaman Boko Haram

Hakkin mallakar hoto Nigeria army
Image caption Rundunar sojin ta ce ta gano kwanson roka da injin walda da tukunyar gas.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta lalata wani wuri da kungiyar Boko Haram ke ƙera makaman roka a garin Bama na jihar Borno.

A wata sanarwa da ya fitar, kakakin rundunar soja ta bakwai da ke Borno, Tukur Ismail Gusau, ya ce dakarunsu sun kama wani shugaban 'yan kungiyar Boko Haram mai suna John Trankil.

Ya ce, "An gano kwanson roka da injin walda tukunyar gas a wurin ƙera makaman".

Ya kara da cewa 'yan Boko Haram sun gina wurin ƙera makaman ne da kayayyakin da suka sace daga dakin gwaje-gwajen kimiyya na wata makaranta da ke Bama.

A kwanakin baya ne kungiyar ta Boko Haram ta wallafa wasu hotuna da ta ce ma'aikatar ƙera makamanta ne.