BH: An lalata fiye da makarantu 1,000

Image caption Makarantu fiye da 1,000 aka lalata a kasashen yankin tafkin Chadi sakamakon rikicin Boko Haram

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a yankin Sahel, Toby Lanzer, ya ce mayakan kungiyar Boko Haram sun lalata makarantun da aka kiyasata yawansu da 1,100 a wannan shekarar.

Mista Lanzer, wanda ya zamo jakadan Majalisar a yankin tun a watan Yuli, ya ce makarantun da aka lalata din sun hada da na kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Najeriya.

Lanzer ya kuma bayar da adadin mutanen da rikicin ya raba da muhallansu sakamakon rikicin.

Ya ce yawan al'ummar da ke cikin birnin Maiduguri a yanzu ya kai miliyan biyu da 600,000 sakamakon tururuwar kimanin mutane miliyan daya da 600,000 da suke neman mafaka.

Jakadan ya kara da cewa "koda yake a yanzu haka 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram ba sa cikin masu rura wutar rikicin 'yan gudun hijirar Turai, nan gaba lamarin zai sauya in har rikicin yankin Tafkin Chadi ya ci gaba da ta'azzara."

Kasashen Najeriya da Kamaru da Nijar da Chadi dai na kokarin murkushe kungiyar Boko Haram, wadda hare-harenta ya hallaka mutane da dama a kasashen.