Paris: Ana bincike kan wani dan Morocco

Hakkin mallakar hoto Policia de Francia
Image caption Hukumomi sun ce Salah Abdeslam yana da hannu a hare-haren.

Rahotanni sun nuna cewa binciken da ake gudanarwa kan hare-haren da aka kai a birnin Paris na mayar da hankali ne kan wani dan kasar Belgium wanda asalinsa dan Maroko ne, a matsayin wanda watakila ya shirya kai hare haren.

Abdulhamid Abaaoud, mai shekaru 27 na zaune ne a wata anguwa da birnin Brussels kamar biyu daga cikin maharan.

Hukumomin Faransa sun ce sun iya tantance karin mutane biyu daga cikin maharan.

An kai samame a wurare 168

'Yan sandan kasar sun kai samame a wurare 168 a sassan kasar daban-daban bayan harin da aka kai a birnin Paris ranar Juma'a.

Ministan harkokin cikin gida, Bernard Cazeneuve, ya shaida wa manema labarai cewa an yi wa mutane 104 daurin-talala.

Kazalika, an kama mutane 23 domin yi musu tambayoyi.

A cewar sa, an kwato makamai, cikinsu har da bindigogi kirar Kalashnikov da bindigogi masu sarrafa kansu da kuma bindigogin da ke harbo jiragen sama.

Gwamnatin Faransa ta ce tana amfani da damar da ta samu bayan sanya dokar ta-baci domin yi wa mutanen da ke da alaka da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi tambayoyi.

An kitsa hare-haren daga Syria

Firai Ministan Faransa, Manuel Valls, ya ce an kitsa hare-haren da aka kai a birnin Paris ne a kasar Syria.

Mr Valls ya kara da cewa 'yan sanda sun kai samame a wurare fiye da 150 a duk fadin kasar a yayin da ake ci gaba da yin bincike kan hare-haren da aka kai a kasar ranar Juma'a.

Ya bayyana haka ne a yayin da hukumomin tsaron kasar suka fara neman mutanen da suka rage a raye a cikin wadanda suka kitsa hare-haren.

Hare-haren dai sun yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 129 a birnin Paris.

'Yan sanda sun ce wani matashi dan shekaru 26 mai suna Salah Abdeslam, haifaffen birnin Brussels na da hannu a kai hare-haren.

Sun ce gabanin kai hare-haren, an taba tsayar da shi a wajen binciken abubuwan hawa, sai dai an bar shi ya tafi.

Kazalika, Faransa ta kaddamar da hare-hare a yankunan da ke hannun 'yan kungiyar IS mai ikirashin kishin Musulinci a kasar Syria.

Haka kuma, rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa 'yan sanda sun gudanar da bincike yankin Bobigny da ke wajen birnin Paris.