"Ba zamu sauya taku kan yaki da IS ba"

Image caption Shugaba Obama da sauran takwarorinsa na G20 sun sha alwashin kawar da kungiyar IS

Shugaba Obama ya yi watsi da kiraye-kirayen da ake yi kan ya sauya taku a kan yaki da kungiyar IS.

A wani taron manema labarai bayan kammala taron G20 da aka yi a Turkiyya, Mista Obama ya ce dabarun Amurka za su yi aiki, duk da dai cewar zai dauki lokaci.

Da aka tambaye shi ko zai tura dakarun Amurka domin su kawar da mayakan IS, sai ya ce yin hakan zai zamanto babban kuskure, kuma za a yi nasara a kan hakan ne kawai idan har sojin Amurka za su mamaye lardin din-din-din.

Mista Obama ya kara da cewa "sojin Amurka za su iya shiga garuruwan Mosul da Ramadi da Raqqa kuma za su murkushe mayakan IS, amma kuma za a maimaita abinda ya faru ne a baya."

Shugabannin kasashen duniya a wurin taron sun ce a shirye su ke da su yi duk abinda za su yi domin shawo kan ta'adanci.

Za su yi hakan ne ta hanyar sanya takunkumi a kan harkokin kudi da musayar bayanai tsakanin kasashen G20 da kuma magance hanyar samun kudaden kungiyoyin ta'addanci.