An kara wa MTN wa'adin biyan tara

Hakkin mallakar hoto
Image caption MTN ya ce yana ci gaba da tattaunawa da hukumomin Najeriya.

Kamfanin wayar salula na MTN ya ce hukumomi a Najeriya sun tsawaita wa'adin da suka dibar masa domin ya biya tarar da aka sanya masa.

Hukumar da ke sa ido a kan kamfanonin sadarwa ce ta sanya wa MTN tarar $5.2bn saboda ya ki rufe layukan mutanen da ba su yi rijista da shi ba har wa'adin yin rijistar ya wuce.

Hukumar ta bukaci MTN ya biya tarar ranar 16 ga watan Nuwamba ( yau ke nan).

Sai dai wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta ce, "Muna sanar da masu hannun jari a cikin kamfanin cewa hukumomin Najeriya sun amince su tsawaita wa'adin da suka sanya mana domin mu biya tara har sai mun kammala tattaunawar da muke yi da su".

MTN ya kara da cewa za su ci gaba da tattaunawa da hukumomin Najeriya kan rahin rufe layukan mutanen da kuma yadda za a shawo kan lamarin.