Mallakar fili cikin sauki a Nigeria

Hakkin mallakar hoto dfid

Sashen tallafawa kasashe na Birtaniya, DFID ya shirya taron wayar da kan jama'a kan yadda za a rika mallakar takardun fili cikin sauki a Najeriya.

Sashen, wanda ya hada gwiwa da gwamnatin Kano, sun fara aiwatar da shirin mai suna GEMS3 a jihar ta Kano.

A wata dabara ta isar da sakon ga jama'a, DFID ta mayar da hankali ne kan masu sana'ar wasannin Hausa wato 'yan Kannywood da kuma 'yan jarida.

Matsalar mallakar gona ko fili ko gida dai wata babbar matsala ce da ta jima tana janyo rikice-rikice tsakanin jama'a.