Biritaniya ta fara sasantawa da Rasha

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Davida Cameron na Biritaniya da Mr. Putin na Rasha na tattaunawar sulhu a tsakaninsu.

Firai Ministan Britaniya David Cameron ya yi sabon yunkuri domin warware bambance-bambance da ke tsakaninsa da Rasha kan yunkurin da suke yi na kawar da kungiyar IS Syria.

A wata tattaunawar, kuma a wani bangaren na taron G20 da ake yi a Turkiya, Mr Cameron ya gaya wa shugaba Vladimir Putin cewa hare haren da ake kai wa kungiyoyin 'yan hamayya masu matsakaicin ra'ayi a Syria kuskure ne.

Amma kuma a wani jawabi da ya yi daga baya, ya ce akwai alamomin da ke nuna cewar Rasha tana kara mayar da hanakali kan 'yan kungiyar IS.

Mr Putin ya ce harin da aka kai Paris ya nuna cewar ya kamata Biritaniya da Rasha su hada kai domin kawar da ta'adanci.