Su waye mata 100 na BBC a 2015?

Image caption Wasu daga cikin gwarazan matan duniya 100 da BBC ta yi duba a kansu.

Su waye mata 100 ababen misali?

BBC ta fitar da jerin sunayen mata 100 daga fadin duniya, wadanda suka zama ababen kwatance.

Wannan ne karo na uku da BBC ke shiri na musamman don yabawa da Mata 100 a duniya, wanda aka kirkira domin samawa mata gurbi na kwarai a labaran BBC.

'Yar fim din nan da ta karbi lambar yabo ta Oscar, Hilary Swank, da kuma shahararriyar mai tallata kayan kawa ta Sudan Alek Wek sun yi fice a jerin matan na wannan shekarar.

Jerin sunayen ya kuma kunshi 'yan kasuwa 'yan kasa da shekaru 30 da kuma mata abin buga misali wadanda suka haura shekara 80.

'Tarar aradu da ka'

Mata 100 na BBC na bana sun kuma hada da masu aikin jinya a fagen fama da masu shirya fina-finai kan abubuwan da suke bukata da al'ummarsu da kuma shugabannin kimiyya da siyasa da ilimi da kuma zane-zane.

Daya daga cikin matan, wata mai fafutuka 'yar Argentina Estela de Carlotto, tana aiki domin hada iyaye da 'ya'yansu da aka sace tun a shekarun 1970 lokacin mulkin soji.

Ta sake haduwa da jikanta Ignacio a shekarar 2014.

Masu kananan sana'o'in namu wadanda a iya cewa jikoki ne ga wadancan, sun bayyana mana shirinsu na bunkasa harkokin kasuwancinsu.

Wata 'yar kasuwa a Jamus Antonia Albert, mai shekara 25, da hadin gwiwa ta bude wani shafi na intanet na kasuwanci kan kula da tsofaffi.

Tana shawartar mata "su zamo masu karfin gwiwa da kuma tarar aradu da ka."

Jerin sunayen na mata 100 na BBC, ya hada mata daga bangarori daban-daban, kamar Li Tingting, wata mai rajin kare hakkin mata 'yan madigo a China, da wata ungozoma Eveles Chimala, da wata marubuciyar kagaggun labarai Jana el-Hassan 'yar Labanon da kuma wata mai barkwanci 'yar Amurka Megan Grano.

"Labaran jarumtaka"

Wasu daga cikin matan namu jarumai ne sosai, kamar Neyda Rojas wata malamar addinin kirista 'yar Venezuela, wacce take ziyartar gidajen yarin kasar da suka cika - wadanda kuma suna daga cikin gidajen yari mafi hatsari a duniya.

Za a fara gudanar da shiri kan mata ta hanyar yayatawa a talbijin da rediyo da kuma intanet har na tsawon mako biyu.

A Indiya kuwa matan da zamu baku bayani a kansu sun hada da yaran jihar Maharashtra da ke yammacin kasar, wadanda ake kiransu 'nakusha' wato wadanda ba a so. Mun yi magana da wadansu daga cikin yaran wadanda aka saka su cikin wannan rukuni tun shekaru hudu da suka gabata.

A Burkina Faso mun sadu da matan 'yan ci rani da mazansu suka bar su, wasu na tsawon watanni, wasu kuwa na tsawon shekaru.

Yayin da a Gabas ta Tsakiya, mun zanta da Malalar Syria mai suna Maisoun Almellehan, 'yar shekara 16 wadda take gudun hijira a Jordan, take kuma kokarin karfafa wa yara 'yan gudun hijira gwiwa su yi karatu su kuma je makaranta.

Shirin zai hada da rana guda da za a tafka muhawara kan yadda mata ke kallon kansu da shugabanci da kuma dangantaka a wurare 100 a fadin duniya da suka hada da Albaniya da Kosovo da Samoa da Fiji da Isra'ila da Jamaica da Najeriya da kuma hedikwatar BBC da ke London.

Za a yada shirin Mata 100 na BBC a intanet da tashar talbijin ta BBC da kuma dukkan sauran sassan BBC na wasu harsunan 28 daga ranar 18 ga watan Nuwamba zuwa 2 ga watan Disamba.

Za ku iya shiga tattaunawar a shafin Facebook da Twitter da kuma Instagram tare da amfani da maudu'in #100Women.