"Laifukan intanet babbar barazana ne ga Afrika"

Image caption Dakikoki 15 kacal sun isa mutum ya yi kutse a intanet

Kwararru sun yi gargadi cewa harkokin da gwamnatoci da 'yan kasuwa ke gudanarwa a intanet ka iya fuskantar barazana nan gaba daga masu aikata zamba a intanet a Afrika.

A yayin da mutane ke kara samun hanyoyin amfani da intanet a Afrika, gwamnatoci da harkokin kasuwanci ma na kara samun hanyoyin gudanar da al'amuransu a intanet, amma akwai tambayoyi kan wane irin tsaro shafukan suke da shi yadda ba za a yi musu kutse ba.

Zambar da ake ta hanyar email inda wasu ke aika wa mutane sako suna nuna cewa su 'yan uwan wani shugaban Afrika ne da ya mutu suna kuma tambayar bayanan banki na mutum ya zama ruwan dare, amma yanzu sun sauya dabara.

A yau masu aikata laifuka a intanet basa bukatar samun izini wajen damar samun bayanai, wanda zai yi sanadin satar makudan kudade.

Alal misali, wani rahoto kan tsaron intanet da aka fitar a baya-bayan nan a Kenya ya ce 'yan kasuwa na tafka asarar kimanin dala miliyan 146 a kowacce shekara sakakamakon laifukan da ake tafka wa a intanet.

"Yadda ake kutse"

Wani mai sharhi a kan laifukan da ake tafkawa a intanet a Kenya, mai suna Freddy, ya nuna wa wakilin BBC yadda shafukan intanet da mafi yawan alummar kasar ke amfani da su ba su da kariya.

Da yake gwada masa misali a wani shafin intanet da ba na gaskiya ba, mai sharhin ya nuna wa wakilin BBC yadda za a iya kutse cikin sauki.

Ya ce "yin hakan zai dauke ni tsawon dakikoki 15 ne kacal."

Image caption Cikin lokaci kalilan Freddy ya samu kutsawa wani shafin intanet har ya sauya lambobin sirri.

Kamar yadda ya yi hasashe, cikin dakikoki 15 din kuwa sai gashi ya samu damar kutsawa shafin ya kuma sauya lambobin sirri tare da kuma sanya abubuwan da yake so.

Freddy wanda yana daga cikin mutanen da suka lakanci yin kutse a shafukan intanet, yana bai wa kamfanoni shawara ne tare da kare shafukansu daga masu kutse a maimakon yin amfani da basirarsa ta hanyar da bata dace ba.

Amma yana jin cewa kokarin kare shafukan intanet da ake yi bai wadatar ba.

"A Afrika ta kudu ma bata sauya zani ba"

Jaridar Sunday Times ta Afrika ta kudu ta ruwaito cewa mazambatan intanet sun kaddamar da hare-hare 6,000 a shafukan intanet na bangarorin more rayuwar al'umma da na masu samar da hanyoyin sadarwa da ma al'amuran kasuwanci a watan Oktoba kawai.

A baya-bayan nan ne kasar Afrika ta Kudu ta bude wata cibiya mai kula da laifukan da ake aiwatarwa a intanet a Pretoria babban birnin kasar, domin taimakawa kasuwanci da gwamnati da kungiyoyin fararen hula domin su yi aiki tare don kare afkuwar irin wadannan lamuran.

Wannan al'amari dai yana faruwa a dukkan kasashen Africa kuma hakan ce ta sa karamin ministan tsaro na Afrika ta Kudu David Mahlobo, ya taimaka wajen kirkirar wata kungiya mai suna Africahackon, wadda ta tattara kwararru a kan laifukan da ake aikatawa a intanet daga jami'o'i domin tattauna wa kan yadda za a samar da maslaha kan wannan lamari, ba sai har an jira al'amarin ya karasa tabarbarewa ba.