Faransa da Rasha na ci gaba da kai wa IS hari

Hakkin mallakar hoto b

Kasar Faransa da Rasha na ci gaba da yin ruwan bama-bamai akan kungiyar IS a Syria.

Yanzu haka dai Faransa ta kai harin sama karo na uku a jere a arewacin kasar ta Syria.

Ministan tsaron Faransar, ya ce jiragen yaki guda goma ne suka yi wa matattarar 'yan kungiyar ta IS luguden wuta a Raqqa.

Shugaban Rashar, Vladimir Putin ya ce ya ba wa sojin ruwan kasar da suke a tekun bahar rum umarni da su yi aiki tare da sojojin ruwa na Faransa.