Ko ka san hanyar sadarwar IS?

Hakkin mallakar hoto IS
Image caption Ba a iya bibiyar hanyoyin sadarwar 'yan kungiyar IS.

Tun bayan harin da aka kai a Paris, babban birnin Faransa, gwamnatocin kasashe a duniya suke ta faman yin kira ga kamfanoni masu kere-kere da su fito da wata fasaha wadda za ta ba wa jami'an tsaro damar bibiyar maganganun mutane.

Wani kwararre kan harkar fasahar kirkira, Farfesa Peter Sommer ya shaida wa BBC cewa yadda 'yan kungiyar IS suke tattaunawa da juna ya fi karfin manyan kamfanonin sadarwar.

Ya ce " ba sa amfani da tsarin da kamfanonin suke amfani da shi".

Farfesan ya kara da cewa tsarin sadarwa na SureSpot yana ba wa masu son boye bayanai damar sadarwa.

Shi ma wani kwararren kan aikata manyan laifuka ta intanet, Farfesa Alan Woodward cewa ya yi dabarar boye bayanai ita ce take sanya duk wani kokarin jami'an tsaro na gano masu aikata laifuka, ya tashi a tutar ba bu.

Yanzu haka dai masu son boye bayanai suna amfani ne da tsarin sadarwa na OTR wanda yake ba wa mutanen da suke tattaunawa damar boye kansu.

Mafi yawancin mutane masu rajin yin jihadi ba sa amfani da hanyar sadarwa wadda mutane suke amfani da ita kamar rubuta sakonni ta wayar tafi da gidanka ko kuma ta manhajar Whatsapp.

Hakkin mallakar hoto ISLAMIC STATE
Image caption Masana sun ce kungiyar IS ta shallake tunanin kamfanonin sadarwa.

An dai tabbatar cewa 'yan kungiyar ta IS mutane da suka kware a harkar fasahar zamani musamman idan aka yi duba da irin yadda suke amfani da kafofin sada zumunta na zamani.