Mutanen da suka mutu a Yola sun karu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Harin dai na kunar bakin-wake ne

Hukumomi a Najeriya sun ce biyu daga cikin mutanen da suka jikkata sakamakon harin da aka kai a birnin Yola sun rasu, abin da ya sa adadin wadanda bam din ya kashe ya kai 34.

Jami’in tsare-tsare na hukumar agajin gaggawa ta kasa, Alhaji Sa’ad Bello, ya shaida wa BBC cewa sauran mutanen da suka jikkata a harin bam -- wanda aka kai ranar Talata a wata kasuwar gwari a birnin -- na ci gaba da karbar magani a asibitoci.

Ya kara da cewa ana ci gaba da kula da mutanen.

Wani dan agaji -- wanda ya taimaka wajen kula da mutane da harin ya shafa -- ya shaida wa BBC cewa wani mutum ne ya zo cikin mutane yana raba musu kudi, kwatsam sai wani abu ya fashe.

Ana kyautata zaton cewa bam din a jikinsa yake a daure kuma ya tashi da shi.

Buhari ya sha alwashin murkushe 'yan ta'adda

Shugaba Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan wadanda suka rasu a harin na Yola, sannan ya yi addua'ar Allah ya bai wa wadanda suka jikkata lafiya.

Shugaban kasar ya jaddada aniyarsa ta murkushe 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram.

Ya kara da cewa, "Makiyanmu ba za su taba yin galaba ba. Za mu hada karfi da karfe domin murkushe ta'addanci".