'Yar wasan Hausa, Mai Aya, ta rasu

Image caption Mai Aya ta taka muhimmiyar rawa a fina-finan Hausa.

Allah ya yi wa fitacciyar 'yar wasan kwaikwayon Hausa, Hajiya Hafsatu Sharada wacce aka fi sani da Mai Aya, rasuwa.

Mai Aya -- wacce ke da kimanin shekaru 70 a duniya -- ta rasu ne ranar Talata da safe a gidanta da ke Sharada a birnin Kano.

Masu ruwa da tsaki a harkar fina-finan Hausa sun bayyana alhininsu ga rasuwar Hajiya Mai Aya.

Jarumin fina-finan, Ali Nuhu ya shaida wa BBC cewa, "Mai Aya mutiniyar kirki ce, uwa ga kowa. Ba karamin rashi aka yi ba".

A baya bayan nan Mai Aya ta taka rawa a manyan fina-finai, inda take fitowa a matsayin mai "rikici".

Shi ma Falalu Dorayi, ya ce Mai Aya mace ce mai son kin ka'ida da son ganin an tarbiyanntar da jama'a.

Ya kara da cewa, "Mai Aya tana da ban dariya da raha. Rabon da mu samu mutum mai ban dariya kamar ta tun kafin rasuwar Hajiya Amina Dumba".

Daya daga cikinsu shi ne fim din Hajiya Babba.