Za a sanya wa gidajen mai takunkumi a Nigeria

Dogayen layukan mai
Image caption Dogayen layukan mai

Ministan man fetur na Najeriya Ibe Kachukwu ya umarci hukumar sayar da albarkatun manfetur ta sanya takunkumi kan gidajen man da ke boye mai.

A wata sanarwa da kakakin kamfanin man na NNPC, Ohi Alegbe ya fitar ya ce Mista Kachikwu ya bayar da umarnin ne a lokacin da ya kai wata ziyarar gani da ido zuwa gidajen mai a Abuja, babban birnin kasar.

Sanarwar ta kara da cewa a ranar Laraba ne kuma ministan zai gana da dukkannin masu ruwa da tsaki a harkar mai da dakonsa a Najeriya.

Wasu sassa na Najeriya sun dade suna fama da rashin mai, sai dai a baya bayan nan ne matsalar ta kunno kai a birnin Abuja.