'Yan ta'adda ne suka harbo jirgin Rasha

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mista Bortnikov ya ce an samu wasu abubuwa masu fashewa a tarkacen jirgin da ya fadi.

Shugaban hukumar tsaron Rasha, Alexander Bortnikov, ya ce 'yan ta'adda ne sukar harbo jirgin kasar wanda ya yi hatsari a yankina Sinai na kasar Masar a watan jiya.

Mista Bortnikov ya shaida wa Shugaba Putin cewa an gano wasu abubuwa masu fashewa a tarkacen jirgin da ya fadi.

Dukkanin mutane 224 da ke cikin jirgin dai sun mutu, kuma akasarinsu 'yan kasar Rasha ne da suka je yawon bude ido.

Kungiyar IS da ke ikirarin kishin Musulinci ta dauki alhakin harbo jirgin.

Shugaba Putin ya sha alwashin farauto mutanen da ke da hannu a faduwar jirgin.