An hana cin kasuwar dare a Adamawa

Image caption A ranar Talata da dare ne aka kai harin da ya kashe mutane 34.

Gwamnatin jihar Adamawa a arewacin Nijeriya, ta haramta cin kasuwanni da kuma dafifin jama'a da daddare, tun daga ranar Laraba, domin kauce wa hare-haren bama-bamai na masu tayar da kayar baya.

Wannan matakin ya biyo bayan wani hari ne da aka kai ranar Talata da dare a wata kasuwa a Yola babban birnin jihar.

Hukumomi sun ce wani mutum ne ya yaudari jama'a, ya tara su, yana raba masu kudi, sai kwatsam ya tayar da bam dinsa, da ya yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 34 da kuma jikkata wasu 86.

Kwamishinan watsa labarai na jihar ta Adamawa, Alhaji Ahmad Sajo, ya shaida wa wakilin BBC cewa an yanke shawarar haramta bude kasuwannin da dare ne, a yayin taron Majalisar Tsaro ta jihar a ranar Laraba.