Mutanen da suka mutu a Kano sun karu

Image caption Yadda kasuwar ta zama bayan kai harin.

Hukumomi a jihar Kano a Najeriya sun ce mutane biyu sun kara mutuwa sakamakon harin da aka kai a kasuwar sayar da wayoyin hannu da ke birnin.

Jami'an asibiti sun shaida wa BBC cewa mutanen da suka sake mutuwar na cikin wadanda aka kai asibiti.

Mutanen sama 50 ne suka jikkata.

Rahotannin dai sun ce wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake ne suka kai harin.

Wani dan kasuwar ya shaida wa wakilin BBC cewa ya hango matan sun wuce ta gaban shagonsa, jim kadan bayan hakan kuma sai ya ji karar fashewar bam.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Muhammd Musa Katsina ya ce rundunarsa tana neman wadansu matan hudu da su ma ake zarginsu da hannu a wannan hari.

Bam na farko ya fashe ne a waje yayin da dayan kuma ya fashe a cikin kasuwar.