An kashe barayin shanu a Kano

Image caption Matsalar satar shanu ta zama ruwan dare a Najeriya.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano tace jami'anta sun kashe wasu mutane takwas da ake zargi da satar shanu yayin wata mummunar musayar wuta da barayin a dajin Falgore da ke jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Muhammad Musa Katsina, ya shaida wa BBC cewa an kuma kama wasu mutane 18 din a raye, an kuma kwato sama da shanu 1,000 da kuma makamai da dama.

Kwamishinan ya kuma ce "Masu satar shanun na neman zama wata babbar barazana ta tsaro a kasar."

Matsalar satar shanu na daga cikin matsalolin da ake fuskanta ta fannin tsaro a arewacin Najeriya, hakan kuma na jawo asarar rayuka da dukiyoyi.